06/06/2026
meye ra'yinku akan wanan al a'mari
So ko Cutarwa ? Haɗarin saka hotunan yara a Intanet (Da kuma Mafita !)
Muna saka hotunan ya'yanmu sanye da uniform ko a ranar haihuwa don murna. Amma kun taɓa tunanin waye ke kallon hotunan ?
Kafin ku dora hoton yaronku na gaba, ku sani kuna jefa su cikin haɗari guda biyu :
■ Garkuwa da mutane (Kidnapping): Hoton yaro da uniform yana nuna wa mugaye ainihin inda makarantarsa take a kullum.
■ Satar Bayanai (Identity Theft): Yan damfara na amfani da hotunan yara don buɗe asusun bogi (Fake accounts) don cutarwa.
MAFITA (Yadda za ku nuna murna cikin tsaro):
Ba cewa muka yi ku daina murna ba, amma ku yi hakan cikin wayo:
■ Rufe tambarin makaranta : Kafin ku dora hoto, ku goge sunan makarantar ko lambar gida.
■ Saka Emoji : Idan hoton na public ne, ku rufe fuskar yaron da alamar zuciya don kare fuskarsa daga idon duniya.
■ Tura a "Private" : Ku tura hotunan a WhatsApp Group na yan uwa da kakanni kawai, maimakon kowa ya gani a Facebook.
Farin cikin ya'yanmu abin alfahari ne, amma tsaronsu shi ne kan gaba.