23/12/2025
BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MATASA
Assalamu Alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu.
Cikin girmamawa da jinjina, ina miƙa gaisuwa ta musamman ga ku 'yan uwana matasa maza da mata, masu hangen nesa da burin ganin Najeriya ta zama ƙasa mai cike da zaman lafiya, ci gaba da adalci. Ina yi muku fatan alheri a rayuwa, tare da addu’ar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira.
Yanzu haka guguwar SIYASAR 2027 ta karade ƙasa. Kowa na da ra’ayinsa, kowa na da wanda yake goyon baya, kuma hakan alama ce ta dimokuraɗiyya. Amma ya kamata mu fahimci cewa siyasa ba ya kamata ta zama hanyar raba kawunanmu ba. Siyasa dama ce ta bayyana ra’ayi cikin lumana da girmama juna.
Ya kai ɗan uwana matashi, ka sani cewa rayuwarka na da muhimmanci fiye da kowanne ɗan takara. Kada ka bari wani ɗan siyasa ya yaudare ka da kuɗi ko kayan abinci ya kuma tura ka cikin rikici ko tashin hankali. Ka guji shiga cikin ayyukan da za su iya jefa ka cikin haɗari ko kuma su lalata makomarka.
Kada ka ɗauki makami saboda siyasa. Kada ka sha wani abu da zai gusar da hankalinka har ka aikata abin da zai jefa ka cikin nadama. Ka tuna cewa bayan zaɓe akwai rayuwa, akwai makoma, akwai iyaye da ke jiran dawowarka gida lafiya.
A matsayinka na matashi, kai ne ginshiƙin ƙasa. Ka zama wanda zai kawo sauyi ta hanyar ilimi, fahimta da kyakkyawar mu’amala. Ka guji tsana da ƙiyayya saboda bambancin ra’ayin siyasa. Abokinka na yau ba dole bane ku yi ra’ayi ɗaya. Amma dole ne ku ci gaba da girmama juna da mutunta juna.
Ka yi amfani da damar da kake da ita wajen wayar da kai da kuma sauran matasa. Ka zama mai ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai. Ka kasance mai faɗakarwa, mai nuna gaskiya da adalci. Kada ka bari siyasa ta mayar da kai kayan aiki.
Ina roƙon Allah ya ba mu shugabanni nagari. Shugabanni masu tsoron Allah, masu kishin ƙasa da jin ƙai ga talakawa. Kuma ina roƙon Allah ya kare mu daga fitina da rikice-rikice, ya sa mu zabi shugabanni nagari da za su jagorance mu zuwa ga ci gaba da zaman lafiya.
Matashi, ka tuna cewa rayuwa tana da daraja. Ka kare kanka, ka kare mutuncinka, ka kare ƙasarka. Ka zabi zaman lafiya, ka zabi fahimta, ka zabi gaskiya.
Allah ya sa mu dace. Amin.