12/09/2024
COMPUTING: BANGARORIN KARATU A TSANGAYAR COMPUTING (NA'URA MAI ƘWAƘWALWA) DA BANBANCE-BANBANCEN SU
Nasan mutane diyawa a wasu lokutan s**an shiga rudani akan wane “Course” yak**ata suyi yayin zuwa jami'a ko Polytechnic a sakanin irinsu Software Engineering, Computer Science da sauransu. To INSHA ALLAH yau zanyi bayani akan kowane da banbancin sa da wani. Duk wanda yakaranta sai yayi “Share” dan wasu ma su karu.
1. Computer Science: Wannan bangare ne da ake karantar “Kimiyyar na'ura mai ƙwaƙwalwar” kacokan, a wannan shi'ar komai da ya danganci ita na'urar za'ayi kokarin koyarda kai k**a daga tarihin ta, yadda yafaro, da yadda aka kirkiri ita computer da yadda zakayi amfani dashi da yadda zaka iya kirkirar naka kila.
Manufar: Daya daga cikin manufar da akeso a Computer Science shine a horar da kai kasamu kwarewa a bangaren nazarin matsala da yadda zaka samar da mafita ga wannan matsalar. Yadda ake kirkirar Manhajar Computer da yadda ake gudanar dashi. Wasu daga cikin kosa-kosai da akeyi aciki sune:
* Programming (Python, C++, Java)
* Algorithms and Data Structures
* Operating Systems
* Theory of Computation
* Databases
Banbanci: Shi komai da ya danganci Computar za'a koyar dashi hatta kasuwanci ana dan tabawa.
2. Information Technology: A wannan bangaren ana koyarda mai karatu ne yadda ake tsimi da tatsar bayanai, yadda ake kula dashi da sarrafashi da kuma yadda ake samar da Network a sakanin Organization.
Manufa: Manufar wannan shi'ar shine horar da mutum wajen kula da bayanai (Information) na kasuwanci da sauransu da yadda zaka gyara matsaloli da ke tattare da wadannan da kuma dukkan abin ya danganci harkar bayanan, k**a da Network, Database, Report da sauransu. Wasu daga cikin Kosa-kosai da ake koyarwa aciki sun hada da:
* Networking and Telecommunications
* Information Security
* Database Management
* IT Project Management
* Web and Mobile Development
Banbanci: Anfi mai da hankali kan bayanai da tsaronsu.
3. Software Engineering: Wannan bangaren ana koyarda yadda ake kirkirar manhaja ne (Software), yadda ake tsara shi, da samar dashi da kuma yadda ake kula dashi.
Manufa: Cikin manufar akwai yadda horar da mai karatu yadda zaina tsara manhajar computer ko na waya da kuma yadd zai kula dashi da dabarun gamsar da mai amfani amfaninsa.
Banbanci: Shi anan anfi mai hankali kan software. Wasu kosa-kosai da ake aciki sun hada da:
* Software Design and Architecture
* Software Testing and Quality Assurance
* Agile Development Methods
* Software Project Management
* User Interface Design
4. Cyber Security: Wannan bangare ne da ake karantar tsaron na'ura, yadda za'a kai farmaki ma na'ura da yadda za'a tsare na'urar da bayanai dake cikinsa da yadda ake binciken laifukan da ake aikatawa da na'urar.
Manufa: Horar da mutum yazama Ethical Hacker ko Security Expert ko Bug Hunter.
Banbanci: Shi wannan fannin bakar harkalla ne da farinsa. Wasu daga cikin kosa-kosai da akeyi:
* Network Security
* Cryptography
* Ethical Hacking
* Risk Assessment
* Incident Response
5. Computer Engineering: Wannan ana karantar yadda ake kirkirar gangar jikin Computar ne da kuma wasu na'urar wato (Embedded System). A Computer Engineering anfi mai da hankali ne kan “Hardware” da samar dashi da kuma ayyukansa.
Manufa: Horar da mutum kan yadda za'a iya kirkirar na'urar ma'ana bangaren gangar jikin wato Hardware. Da kuma wasu na'urorin irinsu Drone da sauransu.
Banbanci: Amfi mai hankali kan Hardware anan. Wasu daga cikin kosa-kosai da akeyi akwai:
* Computer Architecture
* Embedded Systems
* Digital Logic Design
* Microprocessors and Microcontrollers
* Signal Processing
Wadannan wasu daga cikine kuma dunkule na fadi banbance banbancen, idan nasamu lokacin akwai wasu ma da zankawo INSHA ALLAH.
– Muhammad Baba Goni (Royalmaster)
12/09/2024.