11/05/2024
PLEASE SHARE THIS MESSAGE TO FRIENDS & FAMILY
AREWA MUFARKA
KALAMAN SHEIKH IBRAHIM EL-ZAKZAKY
Ana Yakar Arewa Ta Fuska Uku, Amma Mutanen Yankin Ba Sa Ganewa- Inji El-Zakzaky.
1-Noma. wadda ita ce tushen arzikin mutanen yankin, yanzu ta gagara, an hana manoma aiki an kore su daga garuruwan su, wanda ya zauna za a kashe shi.
2-Kiwo. Makiyaya an kashe ana kwashe dabbobin su.
3-Kasuwanci. Sufurin kayayyaki ya zama hadari, saboda ayyukan 'yan ta'adda a hanyoyi. Sai gobara a kasuwanni wadda ba ta lafiya bace a rasa mai ya haddasa ta. Dan kasuwa idan yabi hanya a sace shi a nemi kudin fansa, sai dai a kwashe jarin sa a fanso shi ya dawo ba abin juyawa.
Su kuma manyan yankin ba wannan ne ya dame su ba, in dai za a ba mutum mukami shi kenan kawai.
KALAMAN MUHAMMAD MANSUR LAWAL
Ina tare dakai a wannan batun,ya kamata ƴan arewa mufarka daga ɗimautar da muke ciki wallahi tallahi inhar yazama bamu canzaba to akwai gagarumar matsala anan gaba,manyan dayakamata suyi magana ko suɗau mataki gameda al'amarin su bashine gabansuba duk wanda ya ɗan fito yayi farfaganganda aka sami wani dunƙuli akayimasa ko muƙami sai kajishi shiru,to tunda hakane wai mu matasa miye amfaninmune baxamuyi hoɓɓasa wajen ceto yankinmu daga qangiba INNA lillahi wa'inna ilaihi raji'un 💔 wallahi prof.maqari yayi gaskiya duk da kalmar babu daɗi amma gaskiyace yace mu ƴan Nigeria bugaggune Ni kuma naqara dacewa musamman mu ƴan arewa anmaishemu bamusan me mukeyiba mutum ya shekara huɗu akan mulki babu wani abu da ya tsinanamuku kuma in tenure tadawo yazo ko kunya babu yana raba kuɗaɗe da abinci kuma mu amsa sabidda ta tabbata mu BUGAGGUNE wallahi in zamu farka mufarka inhar bahakaba kuwa to muyi tazama acikin qangi ƴaƴan mu da ƙannenmu gobensu taalaalaace WA'IYYAZU BILLAH. Please share.
*Good morning*