Soyayya U'kubar zuci

Soyayya U'kubar zuci Soyayya Wata Abace Mai Saikakiyar Gaske Idan Bakayi Daceba Haka Kuma Bata Tsufa Akullum Dada Sabuntata Akeyi

KYAKYKYAWAN LABARI!!!MANZON ALLAH (S.A.W)YACE 1. Mafi girman haske"(ilimi)" 2. Mafi girman duhu="(jahilci)"3. Mafi girma...
12/09/2019

KYAKYKYAWAN LABARI!!!

MANZON ALLAH (S.A.W)YACE
1. Mafi girman haske"(ilimi)"
2. Mafi girman duhu="(jahilci)"
3. Mafi girman kyauta=(afuwa)
4. Mafi munin zance=(karya)
5. Mafi kyawun zance=(gaskiya)
6. Mafi kusan tuwar al'amari=(tashin al'qiyama)
7. Mafi girman arziki=(wadatar zuciya)
8. Mafi kyawun hali=(kunya)
9. Mafi munin hali=(kisan kai)
10. Mafi kusantar allah=(ibada)
11. Mafi kusantar shedan=(hassada)
12. Mafi kusantar aljanna=(ciyarwa)
13. Mafi kusantar wuta=(rowa).

NIKUMA NACE!!!
1. Mafi Munin Abin Kunya๐Ÿ™ˆ, ( shine ka/ki samu wannan saqon ka/ki qi turama kowa da kowa )
2. (Allah Ya Sa Mudace).

DAN ALLAH TURA ZUWA GA WASU GROUP DAN AMFANA

HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL!!!Birnin Jalingo jihar Taraba babu lafiya, magoya bayan gwamnan jihar Taraba Dariu Ishaku ...
12/03/2019

HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL!!!

Birnin Jalingo jihar Taraba babu lafiya, magoya bayan gwamnan jihar Taraba Dariu Ishaku sun fito murnan tayashi lashe zabe sai s**a juya abin ya koma ta'addanci

Yanzu haka sun fara kone kone da saran musulmai da adduna suna farfasa Masallatai, ko a yanzu da nake wannan rubutun sunyi ta bangaren Nasarawo Junction

Muna kira ga Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaiwa jihar Taraba daukin gaggawa ta hanyar bada umarnin da ya dace

Allah Ka bawa 'yan uwan mu musulmai nasara akan arna abokan gaba na jihar Taraba

27/09/2018

LADAN DA AKE SAMU BAYAN AN GAMA
SADUWA DA IYALI.
------------------------------------------------------
Daga Kubra Usman Habib Kano
An ruwaito cikin littafin shifaโ€™u sudurโ€ cewa
Annabi
(SAW) yace idan mace ta shiga cikin shaanin
hidimar
mijinta ko tayi kwalliya domin neman yardar sa.
ALLAH (SWT) zai rubuta mata lada guda goma
kuma ya daukaka mata darajarta idan mijinta ya
kirata tayimasa biyayya har ta dauki ciki zata
kasance tanada ladan mai yin azumi da salloli
dare kullum a wajen daukaka kalmar ALLAH wato
jihadiโ€.
Aโ€™isha(RA) tace hakika an baiwa mata alheri
masu yawa to menene ku agareku maza?
Sai annabi(SAW) yayi
dariya yace โ€œBabu wani mutum da ya riki hannun
matarsa da nufin yin jimaโ€™i da ita sai ALLAH
(SWT) yarubuta masa kyawawn ayyuka guda
biyar idan yahada wuya da ita yanada lada guda
goma idan ya
sumbacceta (kiss) yanada lada guda ashirin idan
ya sadu da ita ALLAH (SWT) zai bashi ladan da
yafi duniya da abunda yake cikinta idan yatashi
domin
yin wankan (janaba) ruwan wankan bai gudanaba
a wani bangaren jikinsa sai an shafe zunubansa a
kuma daukaka masa darajarsa.
Ana bashi ladan abinda yafi duniya harda abinda
ke cikinta saboda wannan wankan da yayi kuma
ALLAH (SWT) yana
yima malaโ€™ikunsa kirari yana cewa
((โ€˜ku dubi bawanaacikin dare mai sanyi yana
wankan janaba ya
sakankance nine Ubangijinsaโ€ to ina shaida muku
na gafarta masa โ€)).
ALLAH KA BAMU IKON SADUWA DA MAZANMU
NA SUNNA.

05/10/2017

*LOVE STORY ALONE *
_BEST LOVERS WHATSAPP GROUP _
โคโคโคโคโคโคโคโคโคโค
*BURIN ZUCHIYATA NA BAWA SOYAYYA RAYUWATA DOMIN ETA CE TAKE TAPIYAR DA ZUCHIYATA*
๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’›
*A KODA YAUSHE BURINA NAGA MASOYA A CHIKIN PARIN CHIKI DOMIN SOYAYYA ETACE TAKE SAY TA ZUCHIYA KODA KUWA BABU PAHIMTA A TSAKANI*
๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š
*MASOYA MU RIQE SOYAYYA A KO WANE LOAKACHI SO ZAY KAWO MANA DAUKI A SANDA MUKE BUQATA*
๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™
*MU KALLI CHIKIN IDON WANDA MUKE AO MU BAYYANA MASA SOYAYYA SHINE ZUCHIYARMU ZATA SAMU SAUQI*
๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ
*HASKEN SOYAYHA SHINE YAKE HASKAKA MURMUSHIN MU HARTA KAYGA YABAMU SHAUQI A ZUCHIYA WANDA BABU MADADINSHI*
๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค๐Ÿ–ค
*YAUDARA A SOYAYYA KAN HAYPAR DA DAMUWA MAY KASHE NISHADI SANNAN KUMA MAY ZURPAOA ZUCHIYA CHIKIN QUNCHI SANNAN IDAN MUKA YAUDARI MASOYI DA SOYAYYA TABBAS SOYAYYA ZATA RAMA MASA A LOKACHIN DA BAMU SANIBA*
๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”
*KADA KU KARYA ZUCHIYAN WANDA S**A NUPO KU DA SOYAYYA MASOYI SHINE YASAN SIRRIN ZUCHIYA DAMA SANNAN SHINE ZAI TAPIYAR DA SO KAMAR SHINE JIGON SHI*
โฃโฃโฃโฃโฃโฃโฃโฃโฃโฃ
*SO KAN SAKA MASOYA ZUBAR DA HAWAYE AMMA BANA KUNCHI BA NA NISHADI WANDA DUK LOKACHIN DANA TUNA MAY SONA SAY NAYITA PARA'A HARTA KAYGA HAWAYEN DADIN ZAMA DA ETA YA SAUKA DAGA ZUCHIYATA*
๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•
*SOYAYYA KAN SHIGA ZUCHIYA A HANKALI SANNAN DOLE AKAN BATA MASAUKI A ZUCHIYA YAYINDA TA DOSHI NAZARI KO MURADIN RAY A GABA KUMA ETA CE ZATA HASKAKA RAYUWA*
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
*QAUNA ITACE TAYI DAY DAY DA KYAWUN ZUCHIYA AMMA SO YAKAN QARA WA KAUNA NISHADI SON ETA KAUNA KUNYA CE A CHIKIN TA YAYINDA A SO BA KUNYA TO KAUNA BATA TAREDA WANNAN YANAYIN*
๐Ÿ’“๐Ÿ’“๐Ÿ’“๐Ÿ’“๐Ÿ’“๐Ÿ’“๐Ÿ’“๐Ÿ’“๐Ÿ’“๐Ÿ’“
*KAUNA ITACE ADON ZUCHIYA HAKA KUMA ETACE SILAR SAMUN DOREWAR ZAMAN LAPIYA SANNAN QAUNA BATA PITA DAGA ZUCHIYA HAKAN NE YASA KAPIN QAUNA TA SHIGA ZUCHIYA SAY AN DADE ANA KYAUTATAWA SOYAYYA DA GASKIYA DAKUMA DUKKAN PARIN CHIKI DA YA BAYYANA*
๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—
*SOYAYYA BATA HANGEN DALA SAY DAY BURIN CHIKINTA YAKAN PITO DA TSAN TSAR ABINDA YA BOYE GASKIYA CE KO QARYA HAKA SO BAYA SANUWA TA MAGANA AMMA MUKAN BANBAN CE SOYAYYA MAY NAGARTA DA EDO TA _AJI_*
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
*MURMUSHI YAKAN HASKAKA ZUCHIYA YAYINDA MASOYINKA YAKE MAKA SHI DON YAPI KOMAY KAWO DAUKI MUSAMMAN IDAN ANKASANCE A CHIKIN WANI YANAYI WA YAKE NUNA DAMUWA MURMUSHI KADAY YANA DAUKE WANNAN NAUYIN*
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
*SOYAYYA TAKAN SOKI ZUCHIYA HARTAKAY GA TA HAYPAR DA KADAYCHI KUNYA KO JAN AJI YAKAN CHUTAR DA WANDA YAKE YINSHI WAJEN BAYYANA SOYAYYA DON SO BARUWANSHI DA AJI KO ISA KO KUNYA WAJEN PURTASHI DAN SHI SARKINE*
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
*MU SUTURCE SOYAYYAR MU DA KYAUTATAWA DAKUMA NISHADI HAKA SHINE ZAY NUNA MANA HANYAR DA ZAMU BI WADDA ZATA PITO DA AYNIHIN JIN DADIN MU WANDA BAMUSAN INDA YAKE BA SAY MUNBI QAUNA A BAYA TA NUNA MANA SHI*......โ—
_SOYAYYA SARAUNIYA CE DUK ZUCHIYAR DATA TUNKARA DA NIYAR SHIGA DILE TA SAMU HANYA DON GIRMANTA YA WUCE A TOSHE HANYAR WUCEWANTA IDAN DA HALI MU RUNGUMI SOYAYYA KODAKUWA HAKAN BA SON ZUCHIYAR MU BANE IDAN DA HALI MU MIQA RAYUWANMU GA SOYAYYA KODA KUWA ZAMU RASATA HAR ABADA IDAN DA HALI MUSO ME SANMU KODA KUWA HAKAN BAZAY TABBATAR DA CHIKAR BURIN MU BA IDAN DA HALI MU KYAUTATAWA MASOYAN MU KODA KUWA BAKIN CHIKIN MU ZAY BAYYANA DAGA BAYA SUNE ZAU SHARE MANA HAWAYE SO YAYI RANA KENAN IDAN DA HALI MU DAYNA TSIRON SOYAYYA MU BAYYAN ATAWAKKALINMU A FILY TA HAKAN NE ZAMU SAMU DAMAR GANO ASALIN JIN DADIN MU WANDA YAKE A BOYE A QARQASHIN SAKACHIN MU_
~MU GUJI YAUDARA MASOYA BATADA RIBA~

Ina kuke yan mata masu ruwan ido Ku sai mai kudi zaku aura to Ku sani ba auren me kudi shine nasarar rayuwar ki ba. Nasa...
23/09/2017

Ina kuke yan mata masu ruwan ido Ku sai mai kudi zaku aura to Ku sani ba auren me kudi shine nasarar rayuwar ki ba. Nasara a rayuwa shine zabi mafi alheri daga Allah. Ba kya tunanin Allah ya dana miki tarko ki fada? Shine fa HUWARRAQU ZULQUWWTIL MATEEN. Ki dauka ma kin auri mai kudin, wani garanti k**e dashi cewar baza Ku fada cikin talaucin ba bayan ma kun hayyafa alokacin da bukatar kudin tafi yawa. Duk wanda kika amince ki aura saboda kawai yana da kudi to ki San da sani shima ya San don abinda yasa kika yarda ki sani babu abinda zai biyo baya sai wulakanci da cin mutunci daga karshe kuma sai saki ya biyo baya. Kinga bukatar dai bata biya ba. Nasihata anan shine ki so mutum don Allah ba dan abin hannun sa ba. Ki kuma yi addu'a Allah yayi miki zabi mafi Inganci da alheri ba son zuciyarki ba. Ki sani ya ke yar uwa aure ibada ne babu kuma abinda baya jawowa ya jawo Alkhairi ya jawo sharri. Ya jawo daukaka ya jawo kaskanci, ya jawo farin ciki ya jawo bakin ciki, ya fitar dake daga gidan wahala ya kai ki gidan Hutu, ya fitar dake daga gidan Hutu ya kaiki gidan wahala. Ya raba ki da zaman kauye ya dawo dake birni ya dauke ki daga birni ya kai ki kauye shi yasa ya zama ibada. Babu wacce ta isa ta zabarwa kanta alheri haka babu Wanda ya isa ya zabarwa kansa alheri domin babu Wanda ya San gaibu sai Allah. Abinda k**e gani arziki ne a zahiri baki sani ba Ashe bakin talauci ne a bayansa. Abinda k**e gani talauci ne baki sani ba ashe arziki ne. Hakika babu Wanda yake son wahala ko talauci amma kuma babu Wanda yasan inda arzikin yake. Kamar yadda ya San inda talaucin yake.
Yan mata da samari wadanda tukuna basu yi aure ba ayi hattara. A nemi zabin Allah ba abinda rai yake so ba.

๐Ÿ’”๐Ÿ•บ๐Ÿ’”ZURFIN TUNANIN YARIMAN MASOYA๐Ÿ’”๐Ÿ•บ๐Ÿ’”๐Ÿ’˜๐Ÿ•บ๐Ÿ’˜YARIMAN MASOYA๐Ÿ’˜๐Ÿ•บ๐Ÿ’˜DAUSAYIN MASOYA ๐Ÿ’˜๐Ÿ•บ๐Ÿ’˜๐Ÿ’ป08065883047๐Ÿ“ฒ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’˜ Da za'a Bayyana irin Kuncin...
15/08/2017

๐Ÿ’”๐Ÿ•บ๐Ÿ’”ZURFIN TUNANIN YARIMAN MASOYA๐Ÿ’”๐Ÿ•บ๐Ÿ’”
๐Ÿ’˜๐Ÿ•บ๐Ÿ’˜YARIMAN MASOYA๐Ÿ’˜๐Ÿ•บ๐Ÿ’˜DAUSAYIN MASOYA ๐Ÿ’˜๐Ÿ•บ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’ป08065883047๐Ÿ“ฒ
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž
๐Ÿ’˜ Da za'a Bayyana irin Kuncin da Zukata suke shiga a Sanadin Soyayya,Dana Tabbata Al'amura da dama sun canza.
โค Karku Yanke Kauna da Rahamar Ubangiji,Nason Soyayya
Alkhairi ne,Kar kwiyi Kokarin Bakanta Zuciyar da Tarun Sirrika S**a
Boyu acikinta.
๐Ÿ’›Kada Kuyi Sanadiyyar Zubar Hawaye a Idanuwan da Al'umma
da yawa ke Samun Nutsuwa da walwalarsu,A Karshe inayi Muku Tuni Jinkiri ga yafiya yana zamowa Dana sani.
๐Ÿ’š Idan tsautsayi ya kasance Baya wuce ranar Sa,tome za'a kira Qaddara da duk wani Dan Adam Yana da Irin nasa?Idan Tafiya tai
Nisa waiwaye bai cika zama Abun ado acikinta ba.
๐Ÿ’™ Itafa Zuciya anhalicceta da Soyayyar mai kyautata mata,Sannan ba abinda ta tsana irin mai munana mata tare da Kokarin bata damuwa.
๐Ÿ’œ Cututtuka iri-iri ne amma bana tunanin Akwai Mai Zafin Cutar
So,Soyayyar Gaskiya Tamkar Fatalwane Wanda kowa ke yawan
Maganar ta amma kuma Qalilanne s**a Ganta.
๐Ÿ’” Soyayya ta Gaskiya bata Rabuwa da Farin Ciki na har abada,kuma Sannan bata da Karshe Domin Tushe na Gaskiya.
โฃKu sanyawa Junanku Aminci da Kuma Soyayya kawai Ku cigaba da Tafiya,abunda na Fahimta kawai tsakanin Soyayyar 'Da Namiji
da 'Ya mace tilasne,inba haka ba kuma Mutuwa ta wajaba akan Kowanne Daya daga cikinsu.
๐Ÿ’• Duk ranar da wani Masoyi ya Rabu da dayan Masoyinsa,ina da Tabbacin Walwala tayi Bankwana da Rayuwar Wannan Masoyin.
๐Ÿ’ž Abun da ciwo Kaso Mutum ba tare da Wanda kakeso yasan kanayi ba,amma kuma bana tunanin Akwai abunda Yafi ciwo fiye da Kaso Mutum amma ka Kasa samun kwarin Gwiwar furtawa Wanda k**eso Cewa kana son Shi.
๐Ÿ’“ Ubangiji yana Jarabtarmu da Soyayya ta Karya wacce take cikale da Tarin Rudani,daga bisani kuma ya nufemu da samun Soyayya ta Gaskiya Saboda mu fahimci wacce Ni'ima yai mana agaba.
๐Ÿ’– Soyayya tana k**a Zuciyar 'Da Namiji ta hanyar Idanunsa ne,Ita kuma 'Ya Mace tana kamuwane ta hanyar Kunnuwantane.
๐Ÿ’˜ Alokacin da Alaka tai Nisa Tsakanin 'Da Namiji da 'Ya Mace, Wala Allah Mutunci ne a tsakaninka da ita,Idan ya kasance acikin Alakar Akwai Tausayawa tare da kuma kyautatawa juna,Soyayya na iya Samun matsuguni acikin Zuciyar Kowanne daga cikin su.
๐Ÿ’ Yana Iya Daukarka Minti daya Kacal Kaji kana Ra'ayin Mutum,Zai kuma iya Daukarka kwana daya Kaji ka kamu da Son Mutum amma kuma zai Dauki Tsahon Rayuwa kafin ka manta da Mutumin daka kamu da Cutar Son nasa.
๐Ÿ’Ÿ Akoda Yaushe bani da wani Buri face inga kan Masoya sun hadu,Domin Ina Bakin Cikin inda Mutum in dazai raba kan Masoya.
๐Ÿ’”YARIMAN MASOYA NAKE,KARAMINE NI BA BABBA BA๐Ÿ’”
๐Ÿ’•๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’ž๐Ÿ’”
๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”DAUSAYIN MASOYA ๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”08065883047๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

YA KE 'YAR UWA! KAFIN KI ZA'BI MIJIN AURE, YA KAMATA KIYI MA KANKI WADANNAN TAMBAYOYIN :- Shin wannan saurayin don Allah...
14/07/2017

YA KE 'YAR UWA! KAFIN KI ZA'BI MIJIN AURE, YA KAMATA KIYI MA KANKI WADANNAN TAMBAYOYIN :

- Shin wannan saurayin don Allah ka'dai k**e Qaunarsa, ko kuwa saboda wasu dalilai naki na son duniya?

- Shin zaki so ache wannan shine Uban 'Ya'yanki?. Kuma shin zakiyi alfahari aduniya da lahira idan kika haifi 'da (yaro) mai irin halinsa da yanayinsa?.

- Shin wannan saurayin yana da halaye irin na Tsoron Allah? (Yawan tuna Allah, kiyaye dokokinsa, Bin umurninsa, yin abu don neman yardarsa).

- Shin wannan saurayin idan ya zama Mijinki zaija ki zuwa ga Aljannah ne, ko kuwa zuwa ga Azabar Allah??.

- Shin yana Mutunta Mahaifansa da 'Yan uwansa Mata? Idan har yana Mutuntasu to zai mutunta naki. Idan kuma yana wulakantasu to kema sai ya Wulakanta naki.

- Shin yana yi miki zancen batsa awajen hirarku? Ko kuma yana Kokarin ta'ba jikinki? (Idan yana da wannan halin to Ki Gujeshi domin shai'dani ne).

- Shin yaya tarbiyyar gidansu take? Idan gidansu akwai tarbiyyah to zaki ga alamar hakan daga gareshi da kuma Qannensa Mata da Maza.

- Wajen za'bin saurayi kada Zaqin bakinsa ko kyawun adonsa ya rudeki. Mafiya yawan Samari suna amfani da Zaqin bakinsu ne wajen yaudara da amfani da 'Ya'yan Mutane.

Kada ki sa'ba ma Allah don neman yardar Saurayi. Idan kika bama saurayi damar ta'ba jikinki, to lallai Kinci amanar Iyayenki bisa wahalar tarbiyyar da s**a baki.

Kin ci amanar 'Yan uwanki da danginki tunda kin shigo musu da Mummunar Alfasha atsakaninsu. Kin ci amanar Mijin da zaki aura nan gaba.. (Koda shima Mazinacin ne).

Kin ci amanar Zuriyar da zaki haifa nan gaba. Tunda kika aikata zina kin gurbata Musu jini da wannan dau'dar Zinar taki.

Mafi girma kuma ita Amanar Allah da kika ci. Domin dukkan gabobin jikinki ya badasu amana ne agareki don kiyi amfani dasu wajsn neman yardarsa.

Manzon Allah (saww) kuwa yace Koda bayan rasuwarsa ana nuna masa ayyukan al'ummarsa. Shin ba zaki ji kunya ba, ache yaga Zina acikin ayyukanki?.

Wannan Nasiha ce daga Zauren Fiqhu (07064213990) da fatan Allah yasa ta zama dalilin shiriya ga Masu aikata wannan Kaba'irah. Wadanda basu yi kuma Allah shi kiyayemu baki daya. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU

20/05/2017

SAKONNIN SOYAYYA GUDA 10+
{Sadaukarwa Ga Masoya.}
MARUBUCI; Abba Muhd Dan-Hausa.
NA โ€˜DAYA.
Ke k**ar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke maโ€™abocin zaโ€™ki, tabbas kin yi k**a da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.
NA BIYU.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin dโ€™aya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
NA UKU.
Sauda yawan lokaci idanuwana s**an yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya dโ€™aya.
NA HUโ€™DU.
Na kasance maโ€™abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shudโ€™ewa soyayyar ki na kโ€™aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar maโ€™abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina kโ€™aunar ki.
NA BIYAR.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu k**ar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata.
NA SHIDA.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai kโ€™ona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.
NA BAKWAI.
Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar โ€˜yaโ€™yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kudโ€™i.
NA TAKWAS.
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato โ€œINA SON KAโ€ hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.
NA TARA.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bilโ€™adama dโ€™auka, amma karda ki damu zan zo nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke fadโ€™a gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi sakโ€™o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.
NA GOMA.
Abba ne zaune a kan wata farar kujerar roba cikin wani lambu mai dโ€™auke da korayen ciyayi da niโ€™ima mai dadโ€™i, wajen da ya zamo masa wajen hutawar shi a dukkan lokacin da ya fita wajen aiki bayan ya yi aikin ya gaji nanne inda ya saba zuwa ya kirawo matar shi a waya domin jin halin da ta ke ciki tun bayan auren su wanda hakan ba karamin burge matar tashi yake yi ba sannan kuma yana kโ€™ara soyayyar shi a cikin zuciyarta.
Yauma dai k**ar kullum, ya fito da wayar ta shi daga aljihu ya shiga kiranta, k**ar jira ta ke yi dama bugu dโ€™aya ta dโ€™aga, bayan sallama sai kuwa ya shiga cewa da ita
โ€œMatata Uwar โ€˜yaโ€™yana maganin kukana, Salimat a baya kafin mu yi aure na yi tinanin cewa bayan mun yi aure ba zan ke samun kulawa da tarairaya tare da kalaman soyayyar nan ta ki masu dadโ€™i ba, na yi zaton komai zai canja k**ar yadda na ke gani a wasu gidajen auren ashe mu ba haka abun ya ke ba saima abun da ya ci gaba ya kuma sauya sabon salo mai dadโ€™i, Salimat ina son ki, koda aiki nake yi yadda zan dawo gida na tarar da ke kawai na ke yin tinani, kuma koda abinci zan ci ina ci ne kawai saboda na rayu amma ba wai dan ina jin dadin shi ba, ina son ki sanar da ni abun da zan taho miki da shi idan zan dawo gida ki kuma kular min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawar ki ta dawo hannuna.
A.M. โ€˜Dan-Hausa.
.
KALAMAN SOYAYYA.
(Domin Samari Da โ€˜Yammata Da Maโ€™aurata)
MARUBUCI: Abba Muhd โ€˜Dan-Hausa.
NA SAMARI DA โ€˜YANMATA.
Na Maza:
KIN ZARCE SAURAN MATA.
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewaโ€ฆ..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.
SINADARIN RAYUWA TA.
SO shi ne abun da ya dunโ€™kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani dโ€™an โ€˜karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
ZAN SO

*BUDURCINKI JARINKI*Ya ke Yan Uwata Kisani Budurcinki ne Samari suke gani yasasuke binki, Duk lokacin da ki ka mayar da ...
26/03/2017

*BUDURCINKI JARINKI*
Ya ke Yan Uwata Kisani Budurcinki ne Samari suke gani yasa
suke binki, Duk lokacin da ki ka mayar da kan ki k**ar Jaka
s**ayi amfani da ke shikenan budurcinki ya tafi, Kuma
kema sun daina kula ki in ba sa'a ki kayi bama sune zasu
fara kiranki da suna yar iska ko mazinaciya, kar kiyarda
kwadayi kudi ko wani kayan jindadi na duniya yasa ki sayar
da Budurcin ki, Kiyi hakuri da Talauci da rashin jindadi da ki
ke cikinsa komai yana da lokacin Yar Uwata
Allah ya tsaremu da kwadanyi abun duniya
*UMMAHATUL MUMININ*

BURIN ZUCIYA: Dalilai 41 Na Fifikon Farare A Kan Bakaken MataIdan ba a manta ba, an sha tafka mahawara kan fifiko da sir...
08/03/2017

BURIN ZUCIYA: Dalilai 41 Na Fifikon Farare A Kan Bakaken Mata

Idan ba a manta ba, an sha tafka mahawara kan fifiko da sirrin da Bakaken mata suke da su fiye da Farare, inda har da yawa s**a bayyana gamsuwarsu kan nazarin da aka gudanar. A daya gefen kuma, wasu ba su yarda da hakan ba, suna kafa hujja da cewa a jerin halitta, ba a taba samun wadda ta fi Farar mace samun martaba da daukaka ba.
Wani abokin aikina ya turo min da wani nazari da ya gudanar kan hakan, inda ya ce ya gano ita ma dai farar macen tana da wasu baiwa da kebantattun sirruka har guda 41, wadanda watakila za a iya kallonsu.
Kada a manta, wannan raโ€™ayinsa ne, saboda haka kowa yana da damar ya aiko da nasa. Ga yadda ya kalli farar mace:
1. Ana ganin farar mace ta fi ilmi
2. Ta fi fahimtar karatu fiye da saura
3. Ta fi iya wanka, kwalliya da ado
4. Ta fi kula da miji
5. Ta fi kazar-kazar
6. Ta fi iya girki
7. Ta fi nuna tausayi da son โ€˜yanโ€™uwa
8. Ta fi kula da yara da tsabtace su
9. Ta fi kyau da kwalliya
10. Ta fi nuna soyayya tsantsa ga miji da iya sace zuciyarsa
11. Farar Mace ta iya tafiya
12. Ga ta da iya zama da mutane
13. Tana da rikon amana
14. Tana da rikon addini
15. Tana da mujahada, wato juriyar tsayuwar dare
16. Ga ta da tsabta
17. Ga ta da iya sarrafa harshe
18. Ga ta da zumunci
19. Faraโ€™ar farar mace daban ne
20. Natsuwarta abar dubawa ce
21. Bata da girman kai
22. Ba ta da lalaci
23. Ba ta gulmace-gulmace
24. Ba ta da kishi sosai
25. Ba ta wulakanta mutane
26. Ba ta alaka da kawayen banza
27. Ba ta zumudi
28. Ba ta kyashi
29. Ba ta son yawon banza
30. Ba ta zuwa gayyar sodi
31. Ta fi inganci
32. Farar mace tana da kirki
33. Ba ta da nawa kan aikata abu
34. Tana tsananin girmama iyaye
35. Idan ta so yin Daโ€™a, babu wanda ya fi ta
36. Saboda irin yanayinta, ba ta kaunar ganin kazanta
37. Tafi iya kissa
38. Ba ta fada da kishiya, cikin ruwan sanyi take yin galaba
39. Ba ta jiji da kai
40. Ganin kyan dirinta, ba ta raina saura
41. Uwa uba farar mace na sanyaya idanun mijinta.
Wadannan su ne Sirruka 41 da abokin nawa ya aiko mana. Shin kun amince da hakan? Yana da kyau kowa ya aiko da nasa raโ€™ayin, ba tare da yin amfani kausasan kalamai, ko zagi ba. Da fatan an fahimta.

KIZAMO MACE TA KWARAI1- Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.2- Kada ki zama mai k...
16/02/2017

KIZAMO MACE TA KWARAI

1- Aurenki ya zama domin neman yardar ALLAh kikayi ba dan tara abin duniya ba.

2- Kada ki zama mai kwadayi wajen zaben mijin Aure.

3- Ki zabawa 'ya 'yanki uba ta hanyar Auren wanda ki ka yarda da addininsa da dabi'unsa harma da dangantakarsa.

4- Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki.

5- kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki.

6- Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki.

7- Ki zama mai matukar biyayya ga mijinki.

8- Ki zama kwararriya wajen iya kwalliya kala-kala.

9- Ki zama kwararriya wajen iya girki kala-kala.

10- Ki zama kin iya barkwancin magana wajen baiwa mijinki dariya.

11- Kada ki zama mai rainuwa a cikin duk abinda mijinki ya baki.

12- Ki dinga wanke bakinki da safe da yamma da kuma lokacin kwanciya barci.

13- ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki, da sauransu.

14- Ki dinga girmama Iyayan mijinki da 'yan uwansa da abokansa.

15- Kada ki zama mai satar kayan mijinki.

16- Kada ki zama mai satar fita unguwa.

17- Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.

18- Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya baki.

19- ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.

20- ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da safe, rana, dakuma dare.

21- Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.

22- Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al'amari da zaki yi.

23- Kiyi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.

24- Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki, kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a duk lokacin kwanciya.

25- Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.

26- Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.

27- Ki zama mai yawan canza zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.

28- Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.

29- Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke dukkan wani hukunci.

30- Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake yi miki fada ko Nasiha.

31- Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.

32- Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.

33- Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na zuwa unguwa.

34- Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.

35- Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin sirrin dake tsakaninki da mijinki.

36- Idan zaki yiwa mijinki magana kiyi masa da tattaunsan harshe, da murya mai karya zukata.

38- Ki zama kin iya kallo mai nuna alamun sha'awa ko soyayya.

39- Idan kika samu sabani da mijinki ki bashi hakuri ko da kuwa kece da gaskiya.

40- Ki zama mai tattali a cikin dukkan abinda kika mallaka a gidan mijinki.

41- Kada ki zama mai kwauron baiwa dangin mijinki abinda ya umarceki da a basu.

42- Kada ki zama mai yin dare wajan girki.

43- Kada ki zama uwar adashi ba tare da sanin mijinki ba.

44- kada ki zama mai yawan fada da makwabtanki.

45- Kada ki kasance mai yawan zagi ko Ashariya.

46- Kada ki ringa baiwa Iyayanki Labarin laifin da mijinki yake miki.

47- Ki zama mai hakuri da juriya da halayyar Iyayan mijinki da 'yan uwansa.

48- Idan mijinki ya yi miki laifi kada ki nuna masa bacin ranki a gaban iyayanki ko 'yan uwansa.

49- Kada ki ringa daga murya sama idan kuna sa-in-sa da mijinki.

50- Kada ki ringa baiwa 'yan uwan mijinki labarin laifukansa.

51- kada ki ci wani abu da mijinki baya son warinsa misali tafarnuwa.

52- Ki dinga yiwa mahafiyar mijinki Ihsani da 'yan uwansa.

*_TA YAYA MIJINKI ZAI SO KI KAMAR YA HAUKACE?_*Wata hira da ta gabata tsakanin wata tsohuwa yar shekara 50 da yar wata J...
05/02/2017

*_TA YAYA MIJINKI ZAI SO KI KAMAR YA HAUKACE?_*

Wata hira da ta gabata tsakanin wata tsohuwa yar shekara 50 da yar wata Jarida ta fito da sirrikan hakan:

_yarโ€™jarida: Menene sirrun jin dadin zamantakewa tsakaninki da mijinki, Shin kin Kware ne wajen yi masa girki? Ko kuma Kyakyawace ke? ko dai kece uwar Iyalinsa?_

_Tsohuwa: Jin dadin zamantakewa tsakanin Maโ€™aurata dace ne daga Allah, amm mace na bada gudumawa wajen tabbatuwar haka, domin mace na iya maida gidan mijinta cikin walwala k**ar yanda zata iya maidashi cikin kuncin rayuwa._
_ba wai sai da kudi ba domin da yawa daga cikin mata masu kudi suna cikin kuncin rayuwa._
_yawan โ€˜yaโ€™ya ba shi ke kawo jin dadin rayuwa ba domin kuwa akwai macen da take da fiye da mazajen โ€˜yaโ€™ya goma amma kullum cikin damuwa take kai ta iya yiwuwama mijin ya saketa a karshe._
_daddadan Abinci kuwa bashi gida da maigida ke bukata ba da farko, sabo zaka ga mace tun safe har dare ba abin da take sai girki ga iya girkin amma kullum kukanta mijin baya kyautata mata._

_yarโ€™jarida: To Menene Sirrin?_

_tsohuwa: Yayin da ran mijina ya baci shiru nake ina saurarenshi sauraro da ke cike da nutsuwa da nuna nadama akan abin da yake tuhumata dashi ina gyada kaina don nuna cewa ina sauraron bayanansa kuma na yarda dasu. Idan kika yi shirun kada ki kuskura ki rinka nuna masa cewa kece da gaskiya ko ya zalunceki a tuhumar da yake miki sabo da maza suna da mutukar tsikayen yanayi._

_Yarโ€™jarida: Me yasa bazaki fice ba idan ya fara fadan ki kyaleshi._

_tsohuwa: Kar ki kuskura ki yi haka, sai ya ga k**ar gudunshi k**e ko maganganunshi basu dameki ba. Kawai ki yi shiru kina sauraran jawabansa kuma ki nuna yarda a duk abin da ya gaya miki har sai ya sauka daga fushinsa, sannan sai ki fita ki bashi wuri domin a lokacin jikinsa na bukatar ya dan huta kadan._

_Yarโ€™jarida: Daga nan kuma sai yaya? Zaki daina yi masa maganane tsawon kwanaki ko yaya?_

_tsohuwa: Kada ki gwada wannan halin domin kuwa sai ya saba da hakan a karshema ya fara cusguna miki ta hanyoyi daban daban._

_yarโ€™jarida: To Me ya k**ata ayi?_

_tsohuwa: Bayan kimanin awa biyu sai ki yi masa wani abin da zai dan sa abakinsa na sha ko na Taunawa, na tabbata ba zai ki karba ba, a take zaki ji ya fara miki magana cikin taushin murya yana nuna nadama kan yadda yazo ya fada ki da fada, Kai ta yiwu ma ya tambayeki: โ€œKin ji haushin fadan da na fadaki dashi?โ€ sai kice : โ€œaaโ€ ai gaskiyace ka gayamin, kuma bazai sake faruwaba insha Allah._

_Yarโ€™jarida: Kuma kin yarda da hakurin da ya baki?_

_tsohuwa: E mana sabo da ai ni ba sokuwa bace, ta yaya zan gaskatashi yayin da yake cikin fushi kuma inki gaskatashi bayan ya dawo hayyacinsa._

_yarโ€™jarida: Mutuncin ki fa?_

_Tsohuwa: mutuncina shine neman yardar mijina da kyautata zamantakewarmu ni da shi, kuma wane mutunci mace ke dashi mutukar tana tsayuwa gaban mijinta ba tufafi a jikinta, shi kadai yasan sirrukanta da ba wani mahluki da ya sansu sai shi. To ina mutuncin da ya wuce miijinta?_

*Wani mai hikima yace:*
*Da tsuntsu Allah ya halicci mace da Dawisu zata zamo*
*Da kuma Dabbace da a bareyi zaa halicce ta*
*Da kuma kwaroce tabbas da cikin Mallam Fata-Fata zaka ganta.*
*To sai Allah yayita Mutum kuma aka halicceta da kashin hakarkari na hagu domin ta zam kusa da zuciya abar kauna a Matsayin Mata, Uwa, โ€˜Ya, Kanwa ko Yaya.*

*Allah yasa Mata su ji wannan Nasihar hakika zaa rage yawan sake-sake da s**a yi kakagida a cikin al'ummarmu.*
_ya Allah ka zaunar da mu lafiya a gidan mazajenmu ka bamu ikon yi masu biyayya k**ar yarda addini ya koyar_
*AMEEN

Address

Barade A Word Palace Way Jalingo
Jalingo
ISMAEEL

Telephone

8068948654

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Soyayya U'kubar zuci posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Soyayya U'kubar zuci:

Share