31/01/2026
AMSOSHIN TAMBAYOYI BAKWAI (7) DA ƊALIBAI KE YAWAN YI GAME DA JARRABAWAR JAMB
• ZAMU IYA AMFANI DA TSOHON PROFILE CODES ƊINMU WAJEN RIJISTAR JAMB 2026 ?
Eh, Zaku Iya Amfani Da Shi, Muddin An Yi Creating Ɗinsa Ne Daga Shekarar 2021 Zuwa 2025.
• ZAMU IYA SAUYA LAMBAR WAYAR DA MUKA YI AMFANI DA ITA A BAYA ?
A'a, Babu Damar Sauya Lambar Waya. Dole Ku Cigaba Da Amfani Da Lambar Da Kuka Yi Creating Profile Codes Da Ita.
• BAMU DA LAYI, KO ZAMU IYA AMFANI DA LAYIN IYAYENMU WAJEN RIJISTA ?
Eh, Ɗalibai Zasu Iya Amfani Da Kowanne Layi Wajen Creating Ɗin Profile Codes, Koda Basu Ne S**a Yi Wa Layin Rijista Ba. Kawai Dai Akwai Buƙatar Su Tabbatar Cewa Layin Ba Zai Ɓata Ba.
• JARRABAWAR JAMB MOCK DOLE CE GA KOWANNE ƊALIBI ?
A'a, Ba Dole Bace. Mock Jarrabawar Gwaji Ce Kawai Da Ɗaliban Da S**ai Ra'ayi Suke Rubutawa, Kuma Ana Biyan Ƙarin Kuɗi (Naira 1,500), Domin Rubutata.
• ZAMU IYA RIJISTAR JAMB BA TARE DA LAMBAR NIN BA ?
A'a, Babu Dama. Lambar NIN Wajibi Ce Ga Dukkan Wanda Yake Son Rijistar JAMB UTME, Kuma Da Itane Ake Amfani Wajen Creating Ɗin Profile Codes.
• TOH, ZAMU IYA AMFANI DA NIN ƊIN WANI ƊAN UWANMU WAJEN RIJISTA ?
A'a, Wajibi Ne Kowanne Ɗalibi Yayi Amfani Da NIN Ɗinsa Wajen Rijista, Saboda Dukkan Bayanan Da Suke Jikin NIN Ɗin Sune Suke Hawa Kan Registrations Ɗin Ɗalibi Kaitsaye, Kamar Suna, Kwanan Watan Haihuwa, Jiha Da Kuma Jinsi.
• ZAMU IYA SAUYA EMAIL ƊIN DA MUKA SAKA BAYAN REGISTRATION ?
A'a, Ba a Sauya Email - Muddin An Kammala Rijistar JAMB. Dan Haka Akwai Buƙatar Ku Tabbatar Cewa Email Ɗin Da Zaku Yi Amfani Da Shi Wajen Rijista Naku Ne, Kuma Kuna Da Access Da Shi.
FATAN KUN AMFANA.....